Jump to content

Yaren Vagla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Vagla harshe ne na rukunin harsunanGurunsi ( Gur ) na Ghana mai magana da kusan 14,000. Ana magana da shi a wasu al'ummomi da ke kewayen yammacin yankin Arewa, Ghana . Irin waɗannan al’ummomi sun haɗa da: Bole, Sawla, Tuna, Soma, Gentilpe, da Nakwabi. Mutanen da ke jin wannan yare ana kiransu da Vaglas, ɗaya daga cikin ƙabilun ƴan asalin da ke kewaye da wannan yanki na Arewa, waɗanda Turawan Mulkin Mallaka na Biritaniya suka kawo su ƙarƙashin tsarin mulkin Gonja "Gonjaland" a ƙarƙashin Tsarin Mulkinsu.